Sace sanda: An gano sandar majalisa dokoki

Sace sanda: An gano sandar majalisa dokokiMace theft in senate has everything to do with Buhari

Sanarwar ta kara da cewa an jefar da sandar ne sakamakon matakin tsaurara tsaro da jami'an rundunar yan sanda suka yi a Abuja

Rundunar yan sanda sun gano sandar majalisa da wasu yan daba suka sace a zauren majalisar dattawa.

Yan daba sun far ma zauren majalisa ranar laraba 18 ga wata yayin da yan zauren ke gudanar da zama kamar yadda ta saba har suka saci sandar majalisa.

Kamar yadda mataimakin jami'in hulda da jama'a na rundunar SP Aremu Adeniran ya sanar, an gano sandan a daidai yankin city Gate dake nan garin Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa an jefar da sandar ne sakamakon matakin tsaurara tsaro da jami'an rundunar yan sanda suka yi a Abuja.

Sakamakon hargitsin da ya faru a zauren majalisar yan sanda sun kama Sanata Ovie Omo-Agege wanda ake zargi da kawo yan dabar zauren har suka sace sanda.

Related:   Dr. Zakari Yusuf Usman: Babban malamin ABU ya rasu rana daya da zama Farfesa

Shima mataimakin shugaban majalisar Ike Ekwerammadu wanda ya jagoranci zaman a bisa rashin shugaban sa wanda yayi tafiya domin halartar taro a Amurka, ya kai ziyara fadar shugaban kasa inda ya kora ma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo bayanai kan abun da ya faru a zauren majalisa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.