Ovie Omo-agege: An kama dan majalisa da ya jagoranci yan zanga-zanga da suka sace sandar majalisa

Ovie Omo-agege: An kama dan majalisa da ya jagoranci yan zanga-zanga da suka sace sandar majalisaSenator Ovie Omo-Agege

An kama shi Omo-agege a daidai karfe 1:50 yayin da ya dawo zauren majalisar don cigaba da zama

Yan sanda sun kama dan majalia dattawa mai wakilta jihar Delta, wanda ya jagoranci yan zanga-zanga zuwa zauren majalisa inda har suka kwace sandar majalisa.

Sanata Ovie Omo-agege wanda majalisa ta dakatar kan wani laifi ya shigo zauren ta barauniyar hanya tare da tawagar yan zanga-zanga wadanda suka yi awon gaba da sandar majalisar wanda har yanzu ba'a san inda suka tafi da ita ba.

Shigowar su zauren yayin da ake zama ya tayar da hankali inda suka haifar da hargitsi tare da dakatar da zaman da ake yi.

 

Sakamakon sace sanda da aka yi, yan majalisar sun cigaba da zama bayan an kawo ragowar sandar. Yan majalisar sun bukaci yan sanda da jami'an DSS da su gano inda ainihin sandar yake kuma su mayar cikin gaggawa.

Related:   Abun farin ciki: Shugaba Buhari ya sa hannu ga takarda kan kudirin baiwa matasa damar tsayawa takara

An kama shi Omo-agege a daidai karfe 1:50 yayin da ya dawo zauren majalisar don cigaba da zama.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.