Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya mika tambarin yabo ga iyalen Abiola da Fawehinmi

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya mika tambarin yabo ga iyalen Abiola da FawehinmiKola Abiola ya amshi kyautar a madadin iyayen marigayi

An gudanar da bikin a dakin taro dake fadar shugaban a garin Abuja ranar Talata 12 ga watan Yuni

Shugaban kasa Muhammadu buhari ya mika takardar lambar yabo ga iyalen marigayin Alhaji Moshood Abiola da Gani Fawehinmi.

Shugaban yayi hakan ne a garin Abuja ranar talata a bikin karrama yan gwaggwarmayar siyasa da aka shirya a fadar sa.

 

Tun a cikin ranar 6 ga watan yuni shugaban ya sanar cewa zai karrama marigayin bayan ya sauya ranar bikin dimokradiya daga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni mutunta gwaggwarmaya da aka yi a zaben 1993.

Ya karrama tsohon dan takarar kujeran shugaban kasa wanda ake kyuatata zato shi ya lashe zaben da darajar GCFR.

Babban dan dan marigayin Kola Abiola, ya amshi kyautar a madadin sauran iyalen.

Bayan ga haka shugaban ya karrama Baba Gana Kingibe wanda ya tsaya a matsayin mataimakin Abiola da darajar GCON.

A bikin raya wannan kyaututuka, manyan jami'an gwamnati da sauran jama'a masu hannu da shuni a fannoni daban daban sun halarci taron.

Related:   Nicki Minaj Performs in Barbie Pink Bodysuit With Fishnets & Soaring Ankle Boot

Wani abun birgewa da ya faru a wajen taron bikin shine, yadda shugaban kasa ya mutunta matar marigayi Gani Fawehinmi.

 

Yadda hotuna suka bayyana, shugaban ya durkasa domin daukar wani abu da ya fado daga hannun ta duk da cewa sakataren gwamnatin tarayya ya yunkurin wajen daukan abun gabanin shugaban.

Hoton lamarin yayi musababbin abun muhawara a kafafen sada zumunta inda wasu da dama suka yaba abun da shugaban yayi.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.