Jullen Lopetegui: Kwana daya kafin gasar kofin duniya, tawagar Spain ta sallami kocin ta

Jullen Lopetegui: Kwana daya kafin gasar kofin duniya, tawagar Spain ta sallami kocin taJulen Lopetegui

An sallame shi bisa ga amincewa ga yarjejeniyar horas da yan wasan Real Madrid bayan kammala gasar duniya ba tare da sanar da hukumar kwallon kasar

Hukumar kwallon kafa tan kasar Spain ta sanar cewa ta kori jagoran yan wasan kasar Jullen Lopetegui.

Sanarwan ya zo kwana  gabanin fara gasar cin kofin duniya kuma kwana biyu kafin kasar ta kece raini da kasar Portugal.

Kociyar dai ya amshi aikin horas da yan wasan tawagar Real Madrid bayan kammala gasar duniya ranar 12 ga watan yuni a yerjejenya wacce zata sa ya cigaba da horo har tsawon shekara 3.

Kamar yadda shugaban hukumar kwallon kafar Spain,  Luis Rubiales, ya sanar an sallame shi ne bisa amincewa da yayi ga aikin kungiyar Real madrid ba tare da sanar da hukumar ba.

Related:   Ke duniya! Ya caka wa mahaifiyar sa wuka kan dalilin kudin haya

Rubiales ya kara da cewa duk da cewa tawagar yan wasan zasu yi kewar sa, hakan ba zai hanu su mayar da hankali ga wasan su da Portugal.

Akwai rahotanni dake yaduwa a kafafen watsa labarai cewa tsohon dan wasan Real Madrid, Fernandes Hierro zai maye gurbin sa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.