Ibrahim Hassan Dankwambo: Gwamna ya bada umarnin a kama malamin da ya yi silar yanke hannayen almajirinsa

Ibrahim Hassan Dankwambo: Gwamna ya bada umarnin a kama malamin da ya yi silar yanke hannayen almajirinsa
Ibrahim Hassan Dankwambo: Gwamna ya bada umarnin a kama malamin da ya yi silar yanke hannayen almajirinsa

Yaron da malaminsa yayi silar yanke hannayen sa

Gwamnan ya dauki nauyin kudin maganin yaron kuma yace zai dauki nauyin karatunsa

Gwamnan jihar Gombe  Ibrahim Hassan Dankwambo ya bada umarnin na a kamo Malamin wanda ake zargi da laifin azabtar da almajirinsa wanda ya kai har aka yanke hannayen sa.

Makon da ya gabata ne jama’a da dama suka yi Allah-wada gamei da lamarin yaron wanda malaminsa ya janyo masa mummanar lahani a kafafen sada zumunta na zamani.

Hakan ya jawo har mutane da dama suna ta jawo hankalin gwamnatin jihar domin daukan mataki kan lamarin.

A sakon da ya wallafa a shafin sa na twitter gwamna ya nuna jin dadinsa kan yadda jama’a suka jawo hankalinsa game da yaron mai suna Zubairu da ake zargin Malaminsa ya azabtar da shi har ta kai ga an yanke masa hannaye a asibiti.

Yana mai cewa, “Duk da cewa bana gari amma na baiwa kwamshnan shari’a da harkokin mata da su ziyarci yaron a asibitin da yake jinya. Na kuma baiwa kwamishinan umarnin a kamo wanda ke da alhakin yanke hannaye yaron domin ya fuskanci hukunci”.

Ya kuma kara da cewa bayan biyan kudin maganin yaron, zai dauki nauyin karatunsa.

Related:   Pulse Opinion: On the day Abacha died, Molue ride was free

Har wa yau dai jama’a na kira na a kawo karshen almajirancin a arewacin Nijeriya domin kawo karshen kalubalen da yara kanana ke fuskanta yayin almajiranci.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.