Hauwa Maina: Bayan wata daya da rasuwa, fitacciya jaruma ta samu jika

Hauwa Maina: Bayan wata daya da rasuwa, fitacciya jaruma ta samu jikaKannywood actress Hauwa Maina Ugo is dead

Maryam Bukar Hassan ta haihu ne a daren ranar talata 12 ga watan Yuni a garin Kaduna bayan ta dawo gidan kakar ta inda take karban gaisuwar rasuwar mahaifiyar ta.

Diyar fitacciyar jaruma Hauwa Maina ta samar mata jika bayan wata daya da rasuwar ta.

Maryam Bukar Hassan ta haihu ne a daren ranar talata 12 ga watan Yuni a garin Kaduna bayan ta dawo gidan kakar ta inda take karban gaisuwar rasuwar mahaifiyar ta.

Rahotannin sun bayyana cewa diyar ta dawo kaduna ne daga gidan mijin ta dake garin Abuja bayan rasuwar babbar ta.

 

Mariganya ta rasu ne a ranar 2 ga watan Mayu bayan wata rashin lafiya da tayi. Rasuwar ta ya girgiza jama'a da dama a arewa musamman ma abokan aikin ta a masana'antar fim ta kannywood.

Kamar yadda diyar ta wallafa a shafin ta don sanar da farin cikin ta da samun karuwar, Maryam wacce aka fi sani da Alhanislam a Instagram  ta bayyana farin cikin ta bisa ga karuwar da tayi ta kara da cewa mahaifiyar ta so tayi ma jikan ta tozali sai dai kuma ajali ya riske ta.

 

Maijegon ta bayyana wannan haihuwa a matsayin wani babban abin farin ciki da ya same ta a daidai lokacin da ta ke cikin jin zafin rabuwa da mahaifiyar ta.

Related:   World: J.J. Watt offers to pay for funerals of Santa Fe school shooting victims

Kwanaki baya Maryam wacce alakar ta da mahaifiyar ta baya boyewa ta bayyana cewa zata cigaba da amfani da shafin mariganya wajen yin da'awa.

Gabanin rasuwar ta, Hauwa Maina, ta kasance daya daga cikin kashin baya da suka raya masana'antar fim tun ranar da aka kafa ta.

Tayi fice wajen fitowa a matsayin jarumar shiri da kuma shirya fim da kanta tare da bada umarni.

Tayi suna sosai bisa yanayin rawar da take takawa a fim a matsayin uwa ko mai tausayi.

Muna mata Addua, Allah ya jikanta da Rahama. Ita kuma mai jego Allah ya raya kuma Allah ya kara mata lafiya.
 

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.