Gasar cin kofin duniya: Tawagar super eagles sun garzaya Rasha sanye da rigar gargajiya

Gasar cin kofin duniya: Tawagar super eagles sun garzaya Rasha sanye da rigar gargajiyaJohn Ogu, Elderson Echiejile and Odion Ighalo

Yan wasan sun garzaya kasar ne inda zasu gwabza da sauran kasashen duniya a gasar cin kofin duniya wanda za' a fara ranar alhamis 14 ga wata.

Yayin da sauran kasashe ke jawo hankalin da irin shigar da suke yi, yan wasan tawagar super eagles ta Nijeriya basu yi tsakaci ba inda suka garzaya Rasha sanye da riga irin ga gargajiya.

Rigar dai ya birge ganin yadda aka yi mata ado da tambarin mikiya da irin launin tutar Nijeriya.

Yan wasan sun garzaya kasar ne inda zasu gwabza da sauran kasashen duniya a gasar cin kofin duniya wanda za' a fara ranar alhamis 14 ga wata.

 

Gabanin tafitar tasu, tawagar ta yada zango kasar Austria inda suka motsa jiki domin shirya ma gasar.

Super eagles tana rukuni daya da kasar Croatia da Iceland da Argentina kana wasan su na farko zasu kara da Croatia ranar 16 ga wata.

Related:   labari cikin hotuna: Shagalin bikin auren Fatima Dangote da Jamil Abubakar a garin Abuja

 

Cikin shirye-shirye da suka yi ma gasar, Nijeriya ta buga wasannin sada zumunci da kasar DR Congo da Ingila da Czech Republic.

 

A dukannin wasanin da ta buga, bata yi nasarar lashe ko wasa daya ba. Tayi kunnen doki da Congo inda ta tashi 2-1 wasan ta da Birtaniya daga nan kuma Czech tayi nasara da 1-0 wasan a kasar Austria.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.