Dr. Zakari Yusuf Usman: Babban malamin ABU ya rasu rana daya da zama Farfesa

Dr. Zakari Yusuf Usman: Babban malamin ABU ya rasu rana daya da zama FarfesaJami'ar Ahmadu Bello Zaria

Babban malamin mai suna Dakta Zakari yusuf Ibrahim, ya shahara ne a fannin ilimin kimiya ta Physics

Wani shahararren malamin kimiya na jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya rasu jiya laraba bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Babban malamin mai suna Dakta Zakari yusuf Ibrahim, ya shahara ne a fannin ilimin kimiya ta Physics. Yayi kaurin suna a jami'o'in arewa musamman ma a ABU da jami'ar Umaru Musa yar'adua dake katsina.

Kamar yadda majiya suka shaida mana, malamin ya rasu rana daya da tabbatar dashi a matsayin Ferfesa.

Wani dalibin makarantar ya shaida mana cewa, malamin ya fadi ne yayin da yake koyar da darasi wanda sakamakon hakan ake garzaya dashi asibiti wanda daga bisani Allah yayi masa cikawa.

Related:   Gasar cin kofin duniya: Ali Nuhu ya hadu da golan Real Madrid a kasar rasha

Hazikin malamin kafin rasuwar sa shine shugaban sashen ilimin kimiya na ABU.

Yayi karatun digiri dinsa na farko da na biyu a nan ABU a bangaren Physics kana yayi digiri dinsa na uku na PhD a kan fannin Nukiliya.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.