A garin Maiduguri: Yadda Fusatattun yan sanda suka gudanar da zanga-zanga game da rashin biyan alawus

A garin Maiduguri: Yadda Fusatattun yan sanda suka gudanar da zanga-zanga game da rashin biyan alawusPDP calls for investigation into police protest in Borno

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, fusatattun yan sandan sun bayyana bacin ran su ga sufeton rundunar  yan sanda inda suke daga murya wajen furta cewa sufeton yana aikata zamba.

Harkokin kasuwanci ya tsaya cak yayin da wasu fusatattun jam'an rundunar yan sanda suka gudanar da zanga-zanga a garin Maiduguri domin nuna bacin ran su game da rashin biyan alawus da ya kamata su amsa.

Dakarun tawagar "mopol"na rundunar sun mamaye babban titunan garin domin yin kira na a biya su alawus da ya kamace su na tsawon wata bakwai.

Sunyi hakan ne a ranar litinin 2 ga watan Yuli inda suke zargin sufeton yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris, da daga matsayin na-kusa-dashi ba tare da lura da cancanta da yanayin aikin da suka yi.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, fusatattun yan sandan sun bayyana bacin ran su ga sufeton rundunar  yan sanda inda suke daga murya wajen furta cewa sufeton yana aikata zamba.

Daya daga cikin jagororin yan zanga-zangar ya shaida wa manema labarai cewa, bisa ga dalilin rashin biyan su dayawa daga cikin su gaza biyan bukatun iyalen su.

Yan sandan sunce tun da aka dawo da su jihar Borno, basu samu wani abun karamci ko alheri daga shugaban rundunar yan sanda na kasar.

Sunyi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya duba lamarin su kuma ya dau mataki kan yadda sufeton su ke daga matsayin wasu ta barauniyar hanya.

Related:   She-Man: Man who disguises as a woman to defraud men, arrested

Karya ne yan sanda basu yi zanga-zanga

Sai dai rundunar yan sanda karkashin kakakin ya karyata labarin gangamin da dakarun ta suka gudanar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Jimoh Moshood, ya bayyana cewa yan sanda dake jihar Borno basu gudanar da gangami ba domin dukkanin su suna wajen aiki yayin da labarin ya fito.

Sai dai yace wasu daga cikin yan sandan jihar suka garzaya hedkwatar hukumar na jihar domin samun karin bayani game da ranar da za'a biya alawus din su ba wai sun gudanar da zanga-zanga kamar yadda rahotanni suka nuna.

Ya kara da cewa sufeton yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya umarci kwamishnan jihar da ya isar masu cewa nan bada dadewa ba za'a fitar da kudin alawus. Yace hakan zai faru ba tare da bata lokaci tunda an riga an amince da kasafin kudin hukumar.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*


This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.